Sirirya : Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Ta Fara Aiki
Shirin tsagaida bude wuta da kasashen Amurka da Rasha suka cimma ya fara aiki a sassan kudancin kasar Siriya.
Kafofin watsa labaran kasar sun ce shirin ya hada da sassan lardunan Sweida, da Daraa, da kuma Qunaitera.
hukumar dake sa ido kan al'amuran kare hakkin bil adama ta OSDH a kasar ta ce an samu dan sukuni a yankunan uku da shirin tsagaita wutar ya shafa.
Hukumar ta ce dai ba'a ji musayar wuta ba tsakanin bangarorin dake rikici a kasar a jiya Lahadi.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai sakataren harkokin wajen Rasha Sergueï Lavrov, ya bayyana a gun taron kasashe 20 mafiya karfin tattalin arzki a duniya (G20) cewa kasashen Amurka da Rashar sun cimma matsaya game da kawo karshen kaddamar da hare hare a wadannan yankuna.