Karshen Wahala 'Yan Gudun Hijrar Garin Mausil Ya Zo
Jul 11, 2017 12:13 UTC
Shugaban Majalisar Dokokin Iraki Ya Tabbatar Da Kawo Karshen Wahala Na 'Yan Gudun Hijrar Garin Mausil.
A yayin da aka gabatar da shirin sake gina birnin Mausil, Shugaban Majalisar Dokokin kasar ya ce ganin cewa an kawo karshen 'yan ta'addar ISIS, 'yan gudun hijra na iya komawa gidajensu cikin izza da karamci.
A yayin da yake ishara kan Majalisar zartarwar kasar da ya ce ita ce keda hurumin gina buranan kasar,Salim Jaburi Shugaban Majalisar dokokin kasar ta Iraki ya ce mahukuntan birnin Bagdaza tare da abokaninsu na yankin da na kasa da kasa za su yi aiki tare domin sake gina jihar Nainuwa musaman birnin Mausil da 'yan ta'addar na ISIS suka ruguza.
Tags