Saudiyya : Yarjejeniyar Amurka Da Qatar ''Bata Gamsar Ba"
Saudiyya da kawayenta Larabawa sun ce yarjejeniyar yaki da ta'addanci da Amurka da Qatar suka cimma ''Bata Gamsar da su ba".
A sanarwar bai daya da suka fitar kasashen da suka hada Saudiyya, Bahrain, da Hadaddiyar daular Larabawa da kuma Masar sun ce yarjejeniyar ta tsakanin Doha da Washington ba za ta kai ga gamsar dasu ba cewa Qatar da gaske take, hasali ma matsin lambarsu ne kan kasar ta Qatar ya kai ga cimma wannan yarjejeniyar.
Jiya ne dai kasashen Qatar da Amurka suka sanar da cimma yarjejeniyar yaki da ta'addanci a yayin ziyara da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya kai a Doha a cikin ran gadin da ya soma a yankin mai manufar shawo kan rikicin diplomatsiya na tsakanin kasasshen yankin na tekun Pasha.
Kasashen dai da suka katse duk wata hulda da kasar ta Qatar sun ce babu tabas akan yarjejeniyar, don kuwa ko a baya Qatar bata cika alkawuran data dauka ba.
Qatar dai na ci gaba da musunta zarge-zargen da kawayenta ke mata na taimakawa ayyukan ta'addanci.