Isra'ila : An Sallami Babban Limamin Masallacin Qudus
'Yan sanda yahudawan mamaya na Isra'ila sun sallami babban malamin nan mai bada fatawowi a Palastine, kana limamin masalacin Qudus, Sheikh Muhammad Hussain bayan da suka tsare shi na wasu 'yan sa'o'i bayan harin da aka kai a masallacin Qudus a yau Juma'a.
Sheikh Hussain, shi ma ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP ta wayar tarho sallamar shi bayan da ya fuskanci tambayoyi daga hannun 'yan sandan.
Daya daga cikin 'ya yan babban malamin shi ma ya tabbatarwa da masu aiko da rahotanni da sallamar mahaifin nasa ba tare da gindaya masa wasu sharuda ba.
An dai kama malamin ne bayan wani bayani da ya yi na nuna rashin jin dadi da hana gudanar da sallar Juma'a da mahukuntan yahudawa suka yi bayan harin bindiga da aka kai a kan 'yan sanda yahudawan da suke tsaye a kofar masallacin.
Maharan dai uku sun hallaka 'yan sandan Isra'ila biyu, yayin da suma suka yi shahada yayin dauki ba dadin da jami'an saron yahudawa.
Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya yi Allah wadai da harin, a yayin da firaministan Isra'ila ya nemi yahudawa da su kwatar da hankali.