Hamas Ta Yi Kira Zuwa Ga Zanga-Zangar Kare Masallacin Quds
Kungiyar Hamas ta yi kira zuwa ga gagarumar zanga-zanga a yau Juma'a a dukkanin fadin Palastinu.
Tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, kungiyar gwagwarmayar Palastinawa ta Hamas ta yi kira zuwa ga gagarumar zanga-anga a yau Juma'a a dukkanin zirin Gaza da kuma yankunan gabar yamma da kogin Jordan da birnin Quds.
Bayanin ya ce manufar wannan jerin gwano a yau ita ce bayyana wa duniya halin masallacin Quds mai alfarma yake ciki a hannun yahudawa, tare da hana musulmi gudanar da sallar a cikinsa.
Haramtacciyar kasar Isra'ila tare da cikakken goyon bayan Amurka da wasu daga cikin larabawa 'yan amshin shata ga Amurka, tana ci gaba da cin karenta babu babbaka a kan al'ummar Palastine, tare da keta alfarmar wurare masu alfarma.