Ahmad Abu-Ghaid Ya Zama Babban Sakataren Kungiyar Kasashen Larabawa
Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Bada Sanarwa A jiya Alhamis cewa Ahmad
Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Bada Sanarwa A jiya Alhamis cewa Ahmad AbulGhaid shi ne sabon babban sakataren kungiyar. Kamfanin dillancin Laraban reuters ya bayyana cewa a ranar Laraba da ta gabata ce kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar Ahmad Abu Zaida ya bada sanrwan cewa gwamnatin kasar masar ta amince da Ahmad Abul-Ghaid ya zama dan takarar neman kujerar babban sakataren kungiyar kasashen larabawa kuma tana bukatar kasashen 22 su aminshe a wannan matasyin.
A jiya Alhamis ne , bayan tattaunawa na lokaci mai tsawo kasashen suka kada kurai'ar amincewa da Ahmad Abu-Zaida a matsayin wanda zai maye gurbin Nabil Al-Arabi wanda lokacin jagorancinsa ga kungiyar ya kawo karshe.