Kasar Poland Ta Ki Karban Baki Yan Gudun Hijira Musulmi.
Gwamnatin kasar Polanda ta ki amincewa da karban bakin yan gudun hijira daga kasashen gabas ta tsakiya da kuma arewacin Afrika kasancewar galibinsu musulmi ne.
Witold Waszykoski, ministan harkokin wajen kasar Polanda ya bayyana haka ne a lokacinda yake wata ganawa da wata jaridar kasar a makon da ya gabata. Ya kuma kara da cewa, kasar Poland kamar sauran kasashen turai tana cikin rikici sosai dangane da matsalar yan gudun hijira, amma abinda ta tsaiyar a kan wanna lamarin, shi ne cewa ba zata karbi yan gudun hijira daga kasashen gabas ta tsakiya da kuma arewacin Afrika ba.
Gwamnatin kasar Poland dai ba ji dadin yadda siyasar kasashen turai dangane da karban yan gudun hijira daga kasashen waje yake tafiya ba, kuma ta sha nanata cewa kasar Polanda ba za ta amince da ra'ayin shuwagabannin tarayyar Turai na rarraba yan gudun hijirar a tsakaninsu.
Kafin haka dai, Beata shido, priministan kasar ta Polanda ya ce gwamnatinsa ba zata taba amincewa da tsarin tarayyar Turai na rarraba yan gudun hijira a tsakanin kasashen kungiyar ba, ya kara da cewa don hakan wani irin hauka ne wanda kasar Poland ba zata zama amince da shi ba.
A shekara ta 2015 ne kungiyar tarayyar ta Turai, ta amince da wata shawara ta rarraba yan gudun hijira kimani dubu 160 a tsakaninsu a matsayin wata hanya ta warware matsalolin yan gudun hijira wadanda suka fito daga gabas ta tsakiya da kuma nahiyar Afrka na wucin gadi. Amma wasu kasashe daga cikin kungiyar wadanda suka hada da ita Poland, Hungry da kuma Jumhuriyar Ceck sun ki amincewa da wannan shawarar sun kuma dage a kan hakan.
Daya daga cikin dalilan da wanda wadannan kasashe ukku suke bayarwa, na kin amincewa da karban yan gudun hijiraran da, a halin yanzu suke zaune a kasashen Italia da Girka , shi ne cewa karbansu zai lalata tsarin zamantakewar kasashensu.
Sai dai kungiyar Tarayyar ta Turai, bayan hakuri na shekaru biyu, ta kuduri anniyar ladabtar da kasashen ukku, kamar yadda dokokin tarayyar suka tanadar, idan har wadan nan kasashe suka ci gaba da tsayawa kan ra'ayinsu na rashin amincewa da karban rabonsu na bakin.
Kasar Poland tana ganin tilasta mata daukar nauyin wasu yan gudun hijira, yana dai-dai da kwace diyaucin kasar ne yadda take kan gudanar da harkokinta
Amma kungiyar tarayyar Turai kuma, da bakin Dimitris Aramopoulos, kwamishina mai kula da yan gudun hijira na tarayyar ya ce, Duk wata kasa daga cikin kasashen tarayyar ta Turai tana da hakkokinta wadanda dole ne tarayyar ta kare mata su, amma kuma akwai alkawulan da wace kasa da daukarwa tarayyar, wadanda su ma dole da cika su.
A halin yanzu dai gwamnatin kasar Poland tana cikin takurawan kasashen kungiyar don ta amince da abinda kungiyar ta yanke dangane da yan gudun hijirar. Kafin haka dai, majalisar dokokin kasar ta Poland wacce jam'iyyar masu tsananin kishin kasa ta PIS take da rinjaye a cikinta, ta samar da wasu dokoki wadanda suka sabawa wasu kudurorin tarayyar ta Turai, sanadiyyar hakan ne, tarayyar ta yi ca a kan gwamnatin kasar, ta kuma yi barazanar dakatar da kasar Polanda daga bayyana ra'ayinta a cikin lamuran kungiyar kwata-kwata, wannan barazanar ta tilastawa Priministan kasar kin sanya hannu a kan dokokin.
Bayan wannan barazanar ne dai, gwamnatin kasar ta Poland ta sassauto a cikin kwanakin da suka gabata, inda ta bayyana cewa, zata karbi yan gudun hijirar, amma banda musulmi wadanda suka fito daga kasashen gabas ta tsakiya, ko kuma arewacin Afrika. Sai dai, wanin abin lura ita ce, mafi yawan yan gudun hijira kimani dubu 160 wadanda suke jiran makomarsu a kasashen Girka da Italia sun fito ne daga gabas ta tsakiya ko Arewacin Afrika ne .