Gaza : Yara Biyu Sunyi Shahada Sakamakon Harin Sojojin Isra'ila
Rahottani daga Zirin Gasa na cewa yara biyu ne suka yi shahada sakamakon wani hari ta sama da jiragen sojojin yahudawan Israi'la suka kai da safiyar wannan Asabar.
Yaran biyu da suka hada da Israa Abou Khoussa 'yar shekaru shida da kuma dan uwan ta Yassine dan shekara 10 dukkan nin su sun rasu ne bayan harin sojojin Isra'ilan a kauyan Beit Lahiya dake arewacin zirin gaza, kamar yadda wasu majiyoyin asibiti suka tabbatar.
ko baya ga yaran biyu da suka shahada, an samu yaro guda daya jikkata tare da hadasa barna ga gidajen jama'a.
A wata sanarwa da ta fitar rundinar yankin Qassam a zirin na gaza ta ce jinin yaran da aka zubar ba zai tafi a ban za ba.
Ita ma a nata bangare kungiyar Hamas tayi allah wadai da wannan harin tare cewa wani takala ne daga ISrai'la wanda kuma zai iya kara rura wutar rikici a yankin.