Palasdinu: Asibitocin Yankin Gaza Na Cikin Mawuyacin Hali.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i23378-palasdinu_asibitocin_yankin_gaza_na_cikin_mawuyacin_hali.
Ma'aikatar kiwon lafiya ta Palasdinu ta ce; Yankin Gaza ya shiga cikin matsananci hali.
(last modified 2018-08-22T11:30:34+00:00 )
Aug 20, 2017 18:13 UTC
  • Palasdinu: Asibitocin Yankin Gaza  Na Cikin Mawuyacin Hali.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta Palasdinu ta ce; Yankin Gaza ya shiga cikin matsananci hali.

A yau lahadi ne ma'aikatar kiwon lafiyar ta Palasdinu ta sanar da cewa; A yanzu da akwai marasa lafiya 3000 a cikin Gaza wadanda suke da bukatuwa a kai su waje domin samun magani.

Ma'aikatar kiwon lafiyar ta yankin Gaza, ta ci gaba da cewa; matukar ba a fitar da wadannan marasa lafiyar zuwa waje ba, abu ne mai yiyuwa su rasa rayukansu cikin kankanan lokaci.

Kakakin ma'akatar kiwon lafiya na Gaza, ya kuma ce; Babbar matsalar da yankin yake fuskanta ita ce karancin magani da kuma kayan aiki na asibiti.

Shugaban Palasdinwa Mahmud Abbas Abu Mazin ya ki amincewa da a fitar da marasa lafiyar zuwa waje, saboda sabanin da ke tsakaninsa da gwamnati Gaza ta Hamas.