Masar Ta Mayarwa Da Amurka Martani Akan Yanke Taimakon Kudade.
Aug 24, 2017 04:46 UTC
Ma'aikatar harkokin wajen Masar ta bayyana rashin jin dadinta akan matakin Amurka na rage taimakon kudaden da take ba ta.
Bayanin ma'aikatar harkokin wajen Masar din ta ci gaba da cewa matakin na Amurka zai haifar da sakamako maras dadi a alakar kasashen biyu.
Bayanin ya ci gaba da cewa; Mahukuntan Washington ba su da cikakkiyar masaniya akan muhimmancin alakar kasashen biyu da kuma samun zaman lafiya a cikin Masar.
A ranar talatar da ta gabata ne dai ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da dakatar da bada taimakon dala miliyan 195 ga Masar din.
Amurkan ta sanar da cewa dalilin daukar wannan matakin shine rashin samun wani ci gaba ta fuskar kare hakkin bil'adama da kuma demokradiyya.
Tags