Kasar Qatar Zata Maida Jakadanta Zuwa Tehran
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta bada sanarwan cewa jakadanta a birnin Tehran zai koma bakin aikinsa bayan kauracewa na kimanin watannin 20.
Tashar television ta Presstv a nan tehran ta nakalto kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Qatar a wani rubutun da ya yi a shafin yanar gizo na ma'aikatar a jiya Laraba. Kafin haka dai ministan harkokin wajen kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani ya zanta ta wayar tarho tare da takwaransa na JMI Mohammad Javad Zarif inda ya shaida masa hakan.
Kasar Qatar ta janye jakadanta daga birnin Tehran ne bayan wata zanga zangar da mutanen Iran suka gudanar a biranen Tehran da Mashad inda suke All.. wadai da kisan da gwamnatin kasar Saudiaya tayi wa Aya. Namir Baqir Namr babban malamin shia kuma shugabansu a kasar ta Saudia.
A halin yanzu dai Kasar Qatar tana zaman doya da man ja ne da kasar Saudia wacce take zarginta da goyon bayan ayyukan ta'addanci. Ma'aikatar ta kammala da cewa jakadan Qatar zai koma Tehran inda zai ci gaba da cikekken ayyukansa na jakadanci.