Isra'ila Ta Sake Kaiwa Siriya Hari
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i23803-isra'ila_ta_sake_kaiwa_siriya_hari
Rundinar Sojin Siriya ta ce H.K Isra'ila ta kaiwa wani sansanin sojinta hari a a lardin Mesyaf, dake tsakanin birnin Hama da wata tashar ruwa a yammacin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:30:39+00:00 )
Sep 07, 2017 10:36 UTC
  • Isra'ila Ta Sake Kaiwa Siriya Hari

Rundinar Sojin Siriya ta ce H.K Isra'ila ta kaiwa wani sansanin sojinta hari a a lardin Mesyaf, dake tsakanin birnin Hama da wata tashar ruwa a yammacin kasar.

Sanarwar da rundinar ta fitar ta ce an dai kaiwa sansanin hari ne da sanyin safiyar yau Alhamis da makamai masu linzami daga sararin samaniyar kasar Labanon, kuma harin ya yi sanadin mutuwar mutum biyu da kuma hadassa barna. 

Bayanai sun nuna cewa sansanin da aka kaiwa harin wani wuri ne da da dakarun Rasha ke amfani da shi wajen atisaye, sannan kuma ya kunshi wani reshe na cibiyar binciken kimiya ta kasar Siriya.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da H.K.Isra'ila ke amfani da da rikicin da kasar  Siriya ta fada don kai mata hari, bisa dalilai marasa tushe.