Masar Ta Maida Martani Akan Zarginta Da Take Hakkin Bil'adama
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar, ta ce; Rahoton da kungiyar kare hakkin bil'adam ta "Human Right Watch' ta fitar akan azabtar da fursunoni, siyasa ce a cikinsa.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Masar, Ahmad Abu Zaidan, ya fada a yau alhamis cewa; Rahoton da ke cewa; Ana azabtar da fursunoni a cikin tsari a kasar ta Masar, wani sabon salo ne na parpaganda da yada jita-jita.
Rahoton da kungiyar kare hakkin bil'adam ta "Human Right Watch" ta fitar akan Masar, ya zargi 'yan sanda da sojojin kasar da azabtar da fursunonin siyasa akai -akai, kuma da kawai daruruwa da aka batar da su.
Kungiyar kare hakkin bil'adaman ta ce ta yi hira da fursunoni 199 da kuma danginsu da suka tabbatar da cewa an azabtar da su daga tsakanin 2014 zuwa 2016.