Duniya Na Goyon-bayan Dunkulewar Iraki A Matsayin Kasa Guda
Kasashen duniya na ci gaba da goyan bayan dunkulewar Iraki a matsayin kasa daya, bayan da Kurdawan aksar suka kada kuri'ar raba gardama, a wani yunkuri na neman 'yancin kan yankin Kurdistan.
Kiran neman dunkulewar kasar ta Iraki na baya bayan nan shi ne na Amurka, wacce ta bakin sakataren harkokin wajenta Rex Tillerson ta ce bata yi na'am ba da zaben raba gardama na Kurdistan ba.
Dama tun kafin zaben AMurka ta yi gargadin cewa zaben zai iya hadassa zaman dar-dar da kuma jefa al'ummar ta Kurdistan cikin tsaka mai wuya.
Baya ga gwamnatin Iraki, kasashen Turkiyya da Iran da wasu kasashe makwabta sun dauki matakai na mayar da martani.
Har wa yau, Majalisar Dinkin Duniya, da Rasha da wasu kungiyoyin kasa da kasa sun nuna kin amincewa ga 'yancin da yankin Kurdawa ke nema, kana, suna goyon-bayan dinkewar Iraki a matsayin kasa daya tak.