Matan Yahudawa Da Na Palastinawa Sun Yi Maci A Qudus
Dubun dubatar matan Yahudawa da na Palastinawa ne suka yi gangami a manyan titunan birnin Qudus domin yin kiraye kirayen kulla yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu.
Wadanda suka shirya gangamin na jiya Lahadi sun yi kiyasin cewa, a kalla mata dubu 30 ne suka halarci taron jerin gwanon.
Kungiyar mata mai rajin tabbatar da zaman lafiya wato "Women Wage Peace" ce ta shirya taron, kuma shi ne zagayen karshe na gangamin makwanni biyu da kungiyar ta shirya wanda aka fara tun daga ranar 24 ga watan Satumban da ya gabata.
An kafa kungiyar "Women Wage Peace" ne wajen shekaru 3 da suka gabata, don fafutukar tabbatar da zaman lafiya mai dorewa da kuma kawo karshen tashin hankalin dake sanadiyyar zubar da jini a tsakanin al'ummar Yahudawa da Palastinwa.
Mambobin kungiyar kimanin dubu 24 suna bayyana aniyarsu na ci gaba da yin fafutukar har sai an cimma yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa.