Oct 19, 2017 17:06 UTC
  • Palastinu : Babu Mahalukin Da Zai Cilasta Mana Ajiye Makamai_Hamas

Shugaban kungiyar Hamas na zirin Gaza, Yahya Sinouar, ya bayyana cewa babu wani mahaluki a duniya da zai cilasta masu ajiye makamai ko kuma amuncewa da Isra'ila a matsayin kasa.

Kungiyar ta Hamas ta rawaito Sinouar na fadan hakan a yayin ganawa da wani gungun matasa.

Wannan dai na a matsayin maida martani ne ga mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila na cewa ba zasu amunce da yarjejeniyar da kungiyar Fatah da Hamas suka cimma a kwanan baya har sai kungiyar ta Hamas ta ajiya makamai ta kuma amuncewa da Isra'ila a matsayin kasa.

A ranar 12 ga watan nan ne kungiyoyin Fatah da Hamas suka cimma yarjejeniyar sulhu tsakaninsu a birnin Alkahira na kasar Masar.

Bangarorin biyu dake gaba da juna a cen baya sun amunce cewa daga ranar 1 ga watan Disamba mai zuwa kungiyar Fatah ce za ta fara gudanar da harkokin zirin Gaza a maimakon Hamas.

 

Tags