Martanin Ma'aikatar Harakokin Wajen Iraki Game Da Cin Zarafin Amurka
Kakakin ma'aikatar harakokin wajen kasar Iraki Ahmad Al-hajib yayi alawadai da furucin da mai magana da yawun ma'aikatar harakokin wajen Amurka Heather Nauert ya yi na sanya mataimakin babban kwamandan dakarun sa kai na kasar Abu Mahdi Al-muhandis cikin jerin 'yan ta'adda.
Cikin wani jawabi da ya gabatar a daren juma'ar da ta gabata, Ahmad Al-hajib ya jajjada goyon bayansa ga rundunar dakarun sa kai na kasar mai suna hashadu-sha'abi, inda ya tabbatar da cewa rundunar sa kai ta hashadu-sha'abi, runduna ce da ta kasance tare da Sojojin kasar kuma take yaki cikin jarumta domin kakkabe 'yan ta'addar IS daga cikin kasar baki daya, sannan kuma Abu Mahdi Al-muhandis mataimakin babban komandan rundunar ta hashadu-sha'abi mutum ne da ya bayar da gudumuwa mai yawa kuma ya sadaukar da kansa ga kasarsa.
A tsakiyar makon da ya gabata, piraministan kasar Iraki ya mayar da martani game da karyace-karyacen da jami'an gwanatin Amurka keyi game da rundunar sa kai ta hashadu-sha'abi, inda ya tabbatar da cewa wannan runduna ita ce fatan wannan kasa da ma yankin baki daya.
A ranar 26 ga watan Nuwambar 2016 ne, majalisar dokokin kasar iraki ta amince da babban rinjaye da kasancewar rundunar sa kai ta hashadu-sha'abi a hukumance cikin wani bangare na rundunar tsaron kasar, wannan adawa da jami'an Amurka ke nuna wa rundunar sa kai ta kasar Irakin shi ke nuna irin damuwar da Amurkan ta shiga ne game da irin canjin da aka samu na baya-byan nan a kasar Iraki, musaman ma nasarorin da sojoji gami da dakarun sa kai din suka samu wajen kakkabe 'yan ta'addar da'esh daga cikin kasar.
Matakin da al'ummar Iraki ta dauka wajen karfafa matakan tsaro ta hanyar dogaro da dakarun sa kai na kasar ya wargaza shirin da Amurka take da shi na rarraba kasar Iraki, yadda farin jinin Dakarun sa kai na Hashadu-sha'abi ke kara karuwa a tsakanin al'ummar kasar Iraki da yankin da kuma irin nasarorin da suke samu wajen kakkabe 'yan t'addar IS daga cikin kasar ya kara kara harzuka mahukuntan na Amurka, ganin cewa wannan runduna ta taimaka wajen wargaza duk wani shiri da suka yi ta hanyar kirkiro da 'yan ta'addar ISIS a yankin gabas ta tsakiya.
A halin da ake ciki mafi yawa daga cikin al'ummar kasar Iraki na bukatar ficewar sojojin Amurka daga cikin kasar su, Amurka dai ta jibge daruruwan sojojinta a cikin kasar Iraki bisa da'awar yaki da ta'addanci, a cikin irin wannan yanayi babu abin da ya rage ga mahukuntan Amurka face ci gaba da mumunar siyasar su ta hanyar rarraba kawunan al'ummar kasar domin kare sojojinta dake cikin kasar, to sai dai martanin da mahukuntan Iraki suka mayar game da farfagandar karya ta mahukuntan Amurka a cikin 'yan kwanakin nan shi ke nuna irin fadakar da Irakiyawa ke da ita.
Canji baya-bayan da aka samu na a matsayin rashin nasara na yakin farfagandar Amurkawa game da rundunar sa kai na yankin da kuma kokarin yin illa ta hanyar sanya shakku a kansu ta hanya sanya su a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda, jinjinawar da ma'aikatar harakokin wajen kasar Iraki tayi ga mataimakin babban kwmandan na rundunar sa kai na hashadu-sha'abi na tabbatar da wannan lamari.