Masar: An Kai Wa Ofishin 'Yan Sanda Hari A Yankin Sina
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i25236-masar_an_kai_wa_ofishin_'yan_sanda_hari_a_yankin_sina
Majiyar tsaro daga kasar ta Masar ta ce wasu mutane da suke dauke da makamai sun kai hari akan wata motar 'yan sanda a yankin Sinaa ta arewa
(last modified 2018-08-22T07:00:55+00:00 )
Oct 29, 2017 15:33 UTC
  • Masar: An Kai Wa Ofishin 'Yan Sanda Hari A Yankin Sina

Majiyar tsaro daga kasar ta Masar ta ce wasu mutane da suke dauke da makamai sun kai hari akan wata motar 'yan sanda a yankin Sinaa ta arewa

Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ambato cewa; A sanadiyyar harin an kashe 'yan sanda biyu da kuma jikkata wasu 10.

Harin na yau ci gaba ne da hare-haren da ake kai wa jami'an tsaro da sojjin kasar ta Syria. Makwanni uku da suka gabata an kashe jami'an tsaro masu yawan gaske.

Tun bayan kifar da gwamantin Muhammadu Mursi,  a 2013 kasar ta Masar ta fada cikin rashin tsaro, musamman a yankin Sina. Kungiyar Ansaru Baitul Mukaddas mai alaka da Da'esh take kai hare-hare a kasar.