Darul Iftah Masar: Ayyukan Kungiyar Daesh A Internet Ya Ragi
Majalisar bada fatawa ta malaman addini wacce ake kira Darul-Ifta ta masar Masar ta bada sanarwan cewa yawan ayyukan kungiyar yan ta'adda ta Daesh a cikin yanar gizo ya ragu.
Kamfanin dillancin labaran Rasa na kasar Masat ya nakalto majalisar tana bada wannan sanarwa a yau Talata, ta kuma kara da cewa nasarorin da aka yi ta samu, kuma ake ci gaba da samu kan wannan kungiyar a kasashen Siria da Iraqi sun yi tasiri a ruguwar ayyukan kungiyar musamman a fagen daukar sabbin mayaka a shafuffukanta na yanar gizo.
Majalisar ta kara da cewa kungiyar ta Daesh ta yi amfani da kafar sadarwa ta Internet wajen yaudarar matasa a kasashen duniya da dama don yi masu aiki, ammma a cikin watannin da suka gabata, yawan ayyukan wannan kunjgiyar a wadan nan shafuffuka sun ragu, sannan majalisar ta gano cewa wasu masu shafuffukan internet daga cikinsu sun shafesu daga yanar gizo kwata-kwata.