Sa'ad Hariri Ya Bar Saudiya Zuwa Kasar Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i25513-sa'ad_hariri_ya_bar_saudiya_zuwa_kasar_faransa
Bayan kwashe makonni biyu a birnin Riyad, a daren Juma'a piraminstan kasar Labnon da ya yi murabus Sa'ad Hariri ya kama hanya zuwa kasar Faransa
(last modified 2018-08-22T07:01:00+00:00 )
Nov 18, 2017 02:19 UTC
  • Sa'ad Hariri Ya Bar Saudiya Zuwa Kasar Faransa

Bayan kwashe makonni biyu a birnin Riyad, a daren Juma'a piraminstan kasar Labnon da ya yi murabus Sa'ad Hariri ya kama hanya zuwa kasar Faransa

A yayin da ya kama hanyarsa ta zuwa birnin Riyad Sa'ad Hariri ya rubuta a shafinsa na twitter cewa labarin da ake yadawa na cewa an tsare shi a kasar saudiya ba gaskiya ba ne, a safiyar yau Asabar ne Sa'ad Hariri ya isa kasar Faransa, inda kuma a yau din zai gana da shugaban kasar Emanuel Macron a fadar Elize.

Tashar telbijin din LBC ta kasar Labnon ta habarta cewa kafin ficewarsa daga birnin Riyad, Piraministan Sa'ad Hariri ya tattauna da Muhamad bn Salman yarima mai jiran gado na Saudiya.

Kafin hakan dai a ranar Alhamis din da ta gabata, shugaba Michel Aun na kasar Labnon ya tabbata da cewa Sa'ad Hariri zai bar birnin Riyad zuwa birnin Paris na kasar Faransa sannan ya ce yana jiran Hariri ya dawo birnin Beirut  domin tattauanwa a game da makomar gwamnatinsa.

A ranar 4 ga watan nuwamba ne Sa'ad Hariri ya sanar da murabus dinsa daga birnin Riyad na kasar Saudiya, sanarwar da ta zo ba zata ga al'ummar kasar, inda wasu ke ganin cewa tilastawa Hariri ne aka yi ya karanta takadar yin murabus din, hukumomin kasar Labnon sun zargi Saudiya da tsare Hariri tare da tilasta masa yin murabus.