Palasdinu: Hamas Ba Za Ta Taba Kwance Damarar Yaki Ba.
Nov 19, 2017 06:43 UTC
Kungiyar ta Hamas ta ce matukar da akwai mamaya a palasdinu babu yadda za ta kwace makamanta.
Jami'in hukumar asirin palasdinu Majid Faraj wanda ya gana da jagoran kungiyar Hamas ne ya ci gaba da cewa mallakar makamai wani hakki ne na al'ummar Palasdinu, kuma koda an kafa 'yantacciyar kasar Palasdinu, to makaman za su ci gaba da zama na sojojin palasdinu.
Bugu da kari bangarorin biyu sun tattauna akan ganawar da kungiyoyin palasdinawa suka yi a birnin alkahira na Masar da kuma wajabcin ci gaba da aiki da abubuwan da aka cimmawa.
Kungiyoyin Hamas da kuma Fatah sun cimma yarjejeniya akan kafa gwamnatin hadin kan kasa da kuma warware sabanin da yake a tsakanin bangarorin biyu.
Tags