Rashin Lafiyar Sheikh Isa Kasim Na Kara Tsananta
Wata kungiyar kare hakkin bil'adama ta mutanen kasar Bahrain a kasar Britania ta bayyana cewa babban malamin mabiya mazhabar shi'a a kasar Bahrain Sheikh Isa Qasim yana fama da tsananin rashin lafiya a daurin talalan da gwamnatin kasar Bahrain take masa a gidansa.
Tashar television ta Presstv ta nakalto kungiyar mai suna Bahrain Institute for Rights and Democracy (BIRD) a takaice tana cewa, wasu likitoci sun sami damar ziyartar Sheikh Isa Qasim a gidansa a yankin Diraz na birnin Manama suna cewa malamin yana bukatar aikin tiyata na gaggawa don daya daga cikin rashin lafiyan da yake fama da su.
Larabarin ya kara da cewa Shiekh isa Kasam yana fama da hawan jini, cutar suga, yana kuma zubar da jini. Banda haka shekarunsa sun kusan 80.
Ali Al-Aswad tsohon shugana Jam'iyyar Al-wifaq ya bayyana cewa gwamnatin kasar Barain wacce ta hana shi fita daga gidansa itace da alhakin duk halin da malamin yake ciki.
Mutanen kasar Bahrain, wadanda mafi yawansu mabiya mazhabar shia ne suna bukatar dangin Ali khalifa su basu damar shiga cikin harkokin gudanar da kasar kamar yadda kowace kasa take a duniya. Su kuma kawo karshen mulkin kama na sarakunan kasar na tsawon shekara da shekaru, ta yadda sarki zai ci gaba da mulkinsa amma jama'a ne za su yi zaben majalisa da kuma firayi minista wanda zai tafiyar da kasa a siyasance da kuma gwamnatance.