Kasashen Masar Da Rasha Sun Jaddada Muhimmancin Fada Da Ta'addanci
Ministan tsaron kasar Rasha, ya bayyana haka ne a yayin ganawa da shugaban kasar Masar Abdulfattah al-Sisy.
Tashar telbijin din Rasha, ta "Rssia Today" ta ce ministan tsaron kasar Sergey Shoygu ya isa birnin al-kahira, inda ya gana da shugaba Abdulfatah al-Sisiy akan batun fada da ta'addanci.
Shugaban kasar ta Masar,ya shaidawa ministan tsaron kasar ta Rasha muhimmancin yin aiki tare kasarsa domin fada da ayyukan ta'addanci a cikin gabas ta tsakiya.
Shi ma ministan tsaron kasar ta Rasha ya bayyana muhimmancin aiki da kasar Rash da kuma tuntubar juna akan fada da ayyukan ta'addanci.
Shaigo ya isar da sakon ta'aziyya da juyayi daga shugaba vladimir putin zuwa ga takwaransa na Masar din akan harin ta'addancin da aka kai a ranar juma'ar da ta gabata wanda ya ci rayuka da dama.