Bahrain: An Kai Ayatollah Sheikh Isa Qasim Asibiti
(last modified Mon, 04 Dec 2017 13:01:18 GMT )
Dec 04, 2017 13:01 UTC
  • Bahrain: An Kai Ayatollah Sheikh Isa Qasim Asibiti

An kai babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Sheikh Qasim asibiti a safiyar yau, sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

Shafin yada labarai na Lu'alua ya bayar da rahoton cewa, a yau ne iyalan babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Isa Qasim suka dauke shi zuwa asibiti, sakamakon matsalolin ciwon suga da hawan jini mai tsanani da yake fama da su.

Mahukuntana masarautar kama karya ta kasar Bahrain sun bayar da dama ga iyalan malamin da su dauke shi zuwa asibiti a yau, bayan tsare shi cikin gida na tswon lokaci, tare da hana shi ganawa da jama'a.

Al'ummomin kasar Bahrain da ma kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya sun gargadi mahukuntan masarautar kama karya ta Bahrain dangane da makomar malamin, sakamakon hana kai shi asibiti domin duba lafiyarsa, wanda hakan yasa ala tilas masarautar ta bayar da dama daukar malamin zuwa asibiti.

Masarautar kama karya ta Bahrain ta killace gidan shehin malamin ne sakamakon kiran da yake yi ga mahukuntan kasar kan su baiwa kowane dan kasa hakkinsa  a matsayinsa na dan kasa, ba tare da tauye hakkin wani bangare ba.

Fiye da kashi 80% na al'ummar Bahrain dai mabiya mazhabar shi'a ne, yayin da sauran al'ummar kasar kuma sun hada da 'yan sunnah da yahudawa da kuma kiristoci gami da masu addinin zartush, sai kuma wahabiyawa wadanda su ne mafi karanci a kasar wadanda kuma su ne mulkin kasar ta Bahrain tun bayan da turawan Bitaniya suka dora su a kan sarautar kasar, wadda har yanzu Ingila ke da hannu wajen tafiyar da ita.