Abdulmalik al-Huthy: An Murkushe Babban Makirci Akan Al'ummar Yemen
(last modified Mon, 04 Dec 2017 18:50:05 GMT )
Dec 04, 2017 18:50 UTC
  • Abdulmalik al-Huthy: An Murkushe Babban Makirci Akan  Al'ummar Yemen

Babban sakataren kungiyar Ansarullah wanda ya gabatar da jawabi dazu ya tabbatar da kashe Ali Abdallah Saleh sannan ya ce; Rana ce ta musamman kuma ta tarihi domin an murkushe makirci da makarkashiya

Babban sakataren kungiyar ta Ansarullah ya kara da cewa; Manufar makarkashiyar da aka kulla, ita ce dankwafar da al'ummar Yemen a gaban wadanda suke yakarsu daga waje.

Abdulmakil Badruddin al-Huthy ya kuma ce; Kasashen da suke kawo wa Yemen hari, suna fatan ganin mutanen Yemen sun shagalta da fada a tsakaninsu maimakon fuskantar yan mamaya.

Tun da fari, kungiyar ta Ansarullah ta sanar da kashe Ali Abdallah Saleh, a yau, kwanaki biyu bayan da tsaohon shugaban kasar ta Yemen ya kira yi magoya bayansa da su yi wa 'yan huthi tawaye.