Isma'ila Haniyyah: Al'ummar Musulmi Sun Hadu Akan Batun Masallacin Kudus
(last modified Mon, 04 Dec 2017 18:52:55 GMT )
Dec 04, 2017 18:52 UTC
  • Isma'ila Haniyyah: Al'ummar Musulmi Sun Hadu Akan Batun Masallacin Kudus

Ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta bakin shugabansa Isma'ila Haniyyah, ya yi gargadi akan shirin Amurka na maida ofishin jakadancinta zuwa Birnin Kudus.

Isma'ila Haniyyah ya bayyana haka ne  a tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da shugaban kasar Turkiya, Rajab Tayyin Urdugan.

 Haniyyah ya kara da cewa; Amurka tana da manufofi biyu dangane da mayar da ofishin jakadancinta zuwa birnin Kudus. Na farko shi ne bada dama ga haramtacciyar Kasar Isra'ila ta shimfida ikonta akan birnin. Na biyu kuwa shi ne makirci domin dakile fatan palasdinawa akan kasarsu.

A nashi gefen, shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan, ya bayyana damuwarsa matuka akan Kudus, sannan ya bayayna cewa kasara za ta taka rawa domin bashi kariya.

A ranar laraba mai zuwa ne dai ake tsammanin cewa shugaban kasar ta Amurka Donald Trump zai bayyana Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar Kasar Isra'ila.