Matsayin Qudus : Trump Ya Kira Abass Ta Wayar Tarho
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i26045-matsayin_qudus_trump_ya_kira_abass_ta_wayar_tarho
A yayin da duniyar musulmi ke ci gaba da nuna damuwa dangane da shirin Amurka na mayar da brinin Qudus fadar gwamnatin yahudawan mamaya na Is'raila, Shugaba Donald Trump ya kira shugaban Palastinawa Mahmoud Abass ta wayar tarho.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Dec 05, 2017 16:05 UTC
  • Matsayin Qudus : Trump Ya Kira Abass Ta Wayar Tarho

A yayin da duniyar musulmi ke ci gaba da nuna damuwa dangane da shirin Amurka na mayar da brinin Qudus fadar gwamnatin yahudawan mamaya na Is'raila, Shugaba Donald Trump ya kira shugaban Palastinawa Mahmoud Abass ta wayar tarho.

Wata jami'i a gwamnatin Palastine ya tabbatar wa da kamfanin dilancin labaren AFP da tattaunawar saidai ba tare da yin karin haske ba. 

Shirin Amurka na dauke fadar gwamnatin Isra'ila daga Tel Aviv Zuwa birnin Qudus na ci gaba da shan suka daga kasashen musulmi.

Kungiyar kasashen larabawa ta bakin sakatarenta, Ahmed Aboul Gheit, ta fitar da wata sanarwa a yau Talata inda ta yi kashedi akan abunda ta danganta da babban hadari, ba ma a Palastinu ba kawai hatta a yankin gabadayansa.

Dama kafin hakan kungiyar kasashen musulmi (OIC) ta ce, duk wani yunkuri na ayyana birnin Qudus a matsayin fadar gwamnatin yahudawan mamaya na Isra’ila, abu ne dai zai harzuka Musulmi a duniya.

A halin da ake ciki dai shugaba Donald Trump ya jinkirta bayyana matsayinsa dangane da shirin, ko da yake an ce wai hakan ba ya na nufin cewa Trump ya jingine wannan batu baki daya ba ne, domin zai bayyana matsayinsa a wani lokaci nan gaba.