Yau Jumma'a Ranar Nuna Fushi Ne A Kasar Palasdinu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i26139-yau_jumma'a_ranar_nuna_fushi_ne_a_kasar_palasdinu
Tun daga sanyin safiyar yau jumma'a yankunan da dama a kasar Palasdinu sun zama fagen fama tsakanin Palasdinawa da jami'an tsaron HKI.
(last modified 2018-08-22T07:01:06+00:00 )
Dec 08, 2017 08:28 UTC
  • Yau Jumma'a Ranar Nuna Fushi Ne A Kasar Palasdinu

Tun daga sanyin safiyar yau jumma'a yankunan da dama a kasar Palasdinu sun zama fagen fama tsakanin Palasdinawa da jami'an tsaron HKI.

Majiyar labarai daga kasar Palasdinu sun bayyana cewa masu zanga-zanga a yankunan gaza da yamma da kogin jordan da kuma sauyan yankunan Palasdinawa da yahudawan HKI suka mamaye suna ta fafatawa da jami'an tsaron yahudawan, sannan ya zuwa yanzu Palasdinawa kimani 50 sun sun jirauni. 

Shugaban kungiyar HAMAS a yankin Gaza, Isma'ila Hania ya bayyana cewa yau jumma'a rana ce ta nuna fushi ga matakin da gwamnatin shugaba Trump ya dauka na amincewa da birnin Quds a matsayin cibiyar mulkin HKI da kuma shirin maida ofishin jakadancinta daga Telaviv zuwa Quds.

Hania ya bayyana wannan shi ne masomin sabuwar intifada ko kuma gwagwarmaya da yahudawan sahyonia yan mamaya. 

A yau jumma'a ana saran za'a gudanar da zanga-zanga a kasashen da dama , daga ciki harda nan JMI kan wannan matsayin da Shugaban Amurka ya dauka.