Palasdinu : Mutum 10 Suka Yi Shahada, Bayan Matakin Trump Kan Qudus
Dec 17, 2017 11:11 UTC
Hukumomin kiwon lafiya a Palasdinu sun sanar da cewa, mutane a kalla goma ne suka yi shahada, kana wasu kimanin 2,000 suka ji raunuka a ci gaba da zanga-zangar tir da matakin shugaba Trump na Amurka kan Qudus.
Yau dai an shiga kwana goma a ci gaba da zanga-zangar ta yin Allawadai da matakin Trump na ayyana Qudus a hukumance a matsayin babban birnin yahudawan sahayoniya.
Kakakin ma'aikatar lafiya ta Palasdinu, Ashraf al-Qudra, ya ce galibin wadanda lamarin ya rusa da su an harbe su ne da harsashin bindiga, da kuma wadanda suka shaki borkonon tsohuwa na jami'an tsaron Isra'ilar.
A ranar Juma'a da ta gabata kawai, mutum hudu ne suka yi shahada a cewar hukumomin lafiya na Palasdinu.
Tags