Masar: Sojoji Sun Kai Farmaki Akan 'Yan Ta'adda
A jiya litinin ne sojojin kasar ta Masar suka sanar da kai hari akan maboyar 'yan ta'adda a arewacin kasar tare da kashe 10 daga cikinsu.
Kamfanin dillancin labarun gwamnatin kasar Masar ya ce; Sojan kasa tare da na sama ne suka kai harin inda suka kashe 'yan ta'adda 10, takwas daga cikinsu masu matukar hatsari.
Bugu da kari sojojin na Masar sun yi nasarar rusa da tarwatsa maboyar makaman da kuma muggan kwayoyin da 'yan ta'addar suke amfani da su.
Yankin Sina a kasar Masar yana a matsayin cibiyar kungiyoyin 'yan ta'adda, da suke amfani da wajen domin kai hare-hare a sassa daban-daban na kasar.
A cikin shekaru uku na bayan nan sojojin kasar ta Masar sun rika fada da 'yan ta'addar kungiyar Da'esh a cikin yankin. Daruruwan 'yan sanda da sojojin kasar ne dai suka rasa rayukansu.