Masar: Sojoji Sun Kashe Wani Kwamadan Kungiyar 'Yan Ta'adda
Dec 28, 2017 19:01 UTC
Majiyar tsaron Masar ta ce an kashe jagoran kungiyar 'yan ta'adda mai matukar hatsari a yankin Sina
Majiyar tsaron ta Masar ta ce; wanda aka kashe din shi ne kwamandan kungiyar nan ta "Ansaru Baitul Mukaddas" mai alaka da Da;esh.
Yankin Sina ta arewa yana a matsayin cibiyar da kungiyoyi masu dauke da makamai suke amfani da shi domin kai hare-hare a cikin kasar Masar.
Haren-haren da kungiyoyin na 'yan ta'adda suke kai wa a cikin Masar, musamman a cikin yankin na Sina, sun yi sanadin mutuwar daruruwan sojoji da yan sandan kasar ta Masar.
Tags