'Yan Sahayoniya Suna Ci Gaba Da Keta Hurumin Masallacin Kudus
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27493-'yan_sahayoniya_suna_ci_gaba_da_keta_hurumin_masallacin_kudus
Majiyar Palasdinawa ta ce; yahudawa 'yan share-wuri-zauna fiye da 50 suka kutsa cikin masallacin na Kudus bisa kariyar 'yan sahayoniya.
(last modified 2018-08-22T11:31:19+00:00 )
Jan 22, 2018 06:20 UTC
  • 'Yan Sahayoniya Suna Ci Gaba Da Keta Hurumin Masallacin Kudus

Majiyar Palasdinawa ta ce; yahudawa 'yan share-wuri-zauna fiye da 50 suka kutsa cikin masallacin na Kudus bisa kariyar 'yan sahayoniya.

Majiyar ta ci gaba da cewa; 'Yan sahayoniyar sun rika yin zane-zane da rubuce-rubuce a jikin bangayen masallacin na kudus masu kunshe da muzanta musulmi da larabawa.

Hukumar da take kula da wuraren musulunci ta kuma bayyana cewa; " 'Yan sandan haramtacciyar Kasar Isra'ila sun hana magina shiga wani sashe na masallacin domin yi masa kwaskwarima.

Keta hurumin masallacin kudus ya zama ruwan dare a wurin yahudawa 'yan sahayoniya, wadanda suke jiran damar rusa shi.