Kokarin Iran na kara yawan Danyan Man da ake fitarwa
Babban saktaren kungiyar kasashe masu fitar da man fetur wato OPEC ya sanar da cewa kasar Iran na iya kokarinta wajen kara yawan danyan Man fetur din da take fitarwa a ko wata rana.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Abdullahi Al-Badri babban saktaren kungiyar OPEC yayin wani zama da kungiyar ta yi jiya Litinin a birnin Viana inda suka tattaunawa kan yanayin da kasuwar danyan man fetur din ke ciki a kasuwanin duniya ya ce tun bayan da aka dage takunkumin da aka kakabawa Iran, kasar ke kokarin kara yawan danyan man fetur din dake take fitarwa a ko wata Rana kafin ma a kakaba mata takunkumin.
Al-badri ya ce a ranar 17 ga Avrilu mai kamawa, kasashen dake fitar da man fetur na kungiyar OPEC da ma wadanda ba sa ciki za su gudanar da taro a kasar Qatar domin tattaunawa kudirin da ya gamata a dauke ta yadda za a daga farashin danyan Man fetur din a kasuwanin duniya, saidai magabatan Iran tun bayan da aka dage masu takunkumi sun dage wajen kara yawan danyan Man fetur din da suke fitarwa kafin ma a dora masu takunkumin.
Iran dai na fitar da gangar danyan Man fetur million dubu biyu da rabi a ko wata rana kafin a kakaba mata takunkumin zalinci saboda shirin nukiliyarta na zaman lafiya, bayan da aka kakaba mata takunkumin sai adadin ya ragu kasa da million daya.