Masar: Kungiyar Ikhwanul-Muslimin Ta Gargadin Gwamnatin al-Sisy
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27665-masar_kungiyar_ikhwanul_muslimin_ta_gargadin_gwamnatin_al_sisy
Kakakin kungiyar ta Ikhwanul-muslimin Talal Fahamy ne ya yi gargadin saboda matsin lambar da gwamnati take yi wa 'yan adaw.
(last modified 2018-08-22T07:01:20+00:00 )
Jan 26, 2018 15:46 UTC
  • Masar: Kungiyar Ikhwanul-Muslimin Ta Gargadin Gwamnatin al-Sisy

Kakakin kungiyar ta Ikhwanul-muslimin Talal Fahamy ne ya yi gargadin saboda matsin lambar da gwamnati take yi wa 'yan adaw.

Fahmi ya kara da cewa; matsin lamabar da gwmanatin Abdulfattah al-Sisy take yi zai jefa mutane cikin yanke kauna da tura su daukar makamai.

kakakin kungiyar Ikhwan' din ya kuma ce; Hanya guda ta kaucewa taho mu gama a kasar ta Masar shi ne komawa zuwa ga tsarin Demokradiyya.

Abdulfattah al-sisy dai yana shirin sake tsayawa takarar shugabancin kasar karo na biyu, tare da yin matsin lamba ga sauran 'yan takarar.

Jami'an tsaron kasar sun yi awon gaba da janar Sami Adnan mai ritaya kwanaki kadan bayan da ya sanar da tsayawarsa takarar shugabancin kasar.

Za a gudanar da manyan zabuka a kasar ta Masar ne a watan Maris na wannan shekara da ake ciki.