Palasdinu: Daya Daga Cikin Mayakan "Izzuddin Kassam Ya Yi Shahada
Feb 01, 2018 06:58 UTC
Kungiyar Hamas ce ta sanar da shahadar daya daga cikin mayakan Izzuddin Kassam wannda reshenta ne na soja.
Sanarwar ta ce; Mahmud Abdulhayyi al-Safdy ya yi shahada ne a yayin da yake gudanar da aikinsa na jihadi a daya daga cikin ramukan karkashin kasa na 'yan gwgawarmaya.
Har ila yau sanarwar ta yabawa al-Safadi wanda ta ce ya kasance mai sadaukar da kai da kuma gwgawarmaya domin 'yanto da dukkanin palasdinu daga mamaya.
Tags