Isma'ila Haniyyah: Muna Ci Gaba Da Riko Da Tafarkin Gwgawarmaya
Shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas Isma'ila Haniyyah ya ce; Kungiyar ba za ta taba sauya matsayarta akan gwagwamaryama ba saboda wani mataki da gwamnatin Amurka ta dauka
Haniyya wanda ya gabatar da jawabi a masallacin Abyadh da ke sansanin 'yna gudun hijira na Shadhi. a yammacin zirin Gaza, ya ce; Matakin da Amurka ta dauka na mayar da ofishin jakadancinta zuwa birnin Kudus, haka nan kuma shigar da sunansa a cikin jerin 'yan ta'adda ba wani alfanu da zai jawo wa Amurkan.
Haniyyah ya kuma ce; Duk wani matakin da 'yan Sahayoniya za su dauka akan gwagwarmaya, babu abin da zai kara wa masu gwgawarmayar idan ba tsayin daka da turjiya ba.
A ranar 31 ga watan Janairu ne dai Baitulmalin Amurka ya shigar da sunan Isma'la Haniyya a cikin bakin littafin Amurka na wadanda take kira 'yan ta'adda.