Ministan Harkokin Wajen Turkiya Zai Kawo Ziyarar Aiki A Iran
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i28009-ministan_harkokin_wajen_turkiya_zai_kawo_ziyarar_aiki_a_iran
A yau laraba ne ake sa ran isowar ministan harkokin wajen Turkiya inda za gana da jami'an gwamnatin Iran
(last modified 2018-08-22T11:31:23+00:00 )
Feb 07, 2018 12:31 UTC
  • Ministan Harkokin Wajen Turkiya Zai Kawo Ziyarar Aiki A Iran

A yau laraba ne ake sa ran isowar ministan harkokin wajen Turkiya inda za gana da jami'an gwamnatin Iran

Kamfanin dillancin labarun "Iran" ya ambato cewa; A yayin ziyarar ta ministan harkokin wajen Turkiyan zai gana da takwaransa na Iran Muhammad Jawad Zarif da kuma shugaban kasa Dr. Hassan Rauhani.

Bangarorin biyu dai za su tattauna alaka a katsakanin kasashensu da kuma abubuwan da suke faruwa a cikin yankin gabas ta tsakiya.

A cikin shekarun bayan nan kasashen Iran da Turkiya da kuma  Rasha, suna aiki tare domin warware matsalar kasar Syria.