Iran : Shugaba Ruhani Na Ziyarar Kwanaki Uku A Indiya
Shugaba Hassan Ruhani, na Jamhuriya Musulinci ta Iran, ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Indiya.
Ziyarar dai wacce ita ce irinta ta farko da Shugaba Ruhani ya kai a Indiya tun bayan hawansa mulki, na da manufar habaka kasuwanci da kuma musayar fasaha a bangaren makamashi tsakanin kasashen biyu.
Kasashen biyu zasu kuma tattauana batutuwan da suka shafi kasa da kasa da kuma yankin.
Iran da Indiya dai na da kyakkyawar alaka a tsakaninsu, tun daga lokacin da Firaministan India Nerendra Modi ya ziyarci Iran a shekara ta 2016, inda shugabannin biyu suka kaddamar da gina wata tashar jiragen ruwa a Chabahar kudu maso gabashi Iran.
Indiya dai babbar abokiyar cinikin man fetur din Iran ce, ko a lokutan baya da Iran take karkashin takunkumin Amurka.