Iran : Shugaba Ruhani Na Ziyarar Kwanaki Uku A Indiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i28177-iran_shugaba_ruhani_na_ziyarar_kwanaki_uku_a_indiya
Shugaba Hassan Ruhani, na Jamhuriya Musulinci ta Iran, ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Indiya.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Feb 13, 2018 17:01 UTC
  • Iran : Shugaba Ruhani Na Ziyarar Kwanaki Uku A Indiya

Shugaba Hassan Ruhani, na Jamhuriya Musulinci ta Iran, ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Indiya.

Ziyarar dai wacce ita ce irinta ta farko da Shugaba Ruhani ya kai a Indiya tun bayan hawansa mulki, na da manufar habaka kasuwanci da kuma musayar fasaha a bangaren makamashi tsakanin kasashen biyu.

Kasashen biyu zasu kuma tattauana batutuwan da suka shafi kasa da kasa da kuma yankin.

Iran da Indiya dai na da kyakkyawar alaka a tsakaninsu, tun daga lokacin da Firaministan India Nerendra Modi ya ziyarci Iran a shekara ta 2016, inda shugabannin biyu suka kaddamar da gina wata tashar jiragen ruwa a Chabahar kudu maso gabashi Iran.

Indiya dai babbar abokiyar cinikin man fetur din Iran ce, ko a lokutan baya da Iran take karkashin takunkumin Amurka.