An Kashe Yan Ta'adda 4 A Yankin Sinaa Na Kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i28415-an_kashe_yan_ta'adda_4_a_yankin_sinaa_na_kasar_masar
Majiyar jami'an tsaro a yankin Sinaa na kasar Masar ta bada labarin kissan yan ta'adda 4 a yankin a yau Laraba.
(last modified 2018-08-22T07:01:27+00:00 )
Feb 21, 2018 08:16 UTC
  • An Kashe Yan Ta'adda 4 A Yankin Sinaa Na Kasar Masar

Majiyar jami'an tsaro a yankin Sinaa na kasar Masar ta bada labarin kissan yan ta'adda 4 a yankin a yau Laraba.

Tashar talabijin ta al-alam a nan Tehran ta nakalto majiyar jami'an tsaron tana cewa sun kashe yan ta'adda 4 sun kuma kama wasu 112 a wani sumamen da suka kai masu a yankin. 

Sojojin kasar Masar sun fara wani farmaki na musamman kan yan ta'adda a yankin Sinaa tun ranar 9 ga watan Afrilun da ya gabata da nufin korarsu daga yankin gaba daya. 

A bisa wani bayanin da jami'an tsaro a yankin suka fitar ya nuna cewa a cikin kwanaki 10 da suka gabata sun kama mutane 417 wadanda suke tuhuma da a\kasancewa cikin yan ta'adda a yankin.