Sharhi: Hadarin Yaduwar Tsatsauran Ra'ayi A Cikin Kasashen Musulmi
An kammala zaman taron yini uku da aka gudanar a kasar Masar, kan samo hanyoyin yaki da tsatsauran ra'ayi da kuma dakile yaduwarsa a cikin kasashen musulmi.
Taron wanda aka gudanar a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar, ya samu halartar malamai da masana daga kasashe fiye da 50, inda aka gabatar da makaloli kan wajabcin mikewa tsaye domin tunkarar barazanar akidun da suke haifar da tsatsauran ra'ayi, wanda ke kai wasu daga cikin musulmi fadawa cikin ayyukan ta'addanci da sunan suna jihadi.
A cikin bayanin bayan taron da aka fitar, an jaddada wajabcin daukar tsaurara matakai a kan kasashen da suke daukar nauyin 'yan ta'adda kuma suke ba su kariya da fatawowi na aikata ta'addanci da sunan addinin muslunci, da hakan ya hada da har da daukar matakai na shari'a a kansu.
Haka nan kuma bayanin bayan taron wanda ke bayyana mahangar mahalarta taron, ya yi ishara da muhimmancin mayar da hankali ga daukar matakai na wayar da kai kan hakikanin koyarwar musulunci, maimakon takaituwa da daukar matakai na karfi wajen tunkarar tsatsauran ra'ayin addini, domin kuwa tsatsauran ra'ayi ya ginu a kan akida wadda take kai mutum zuwa ga wuce gona da iri a cikin addini.
Da dama daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai a wurin taron, da suka hada da manyan malamai da kuma masana daga kasashen duniya daban-daban, sun bayyana akidar wahabiyanci a matsayin babban tushen tsatsauran ra'ayi da ake haifar da kungiyoyin ta'addanci da sunan jihadi a musulunci. Inda masu irin wannan mahanga suke ganin cewa, matukar dai ba asamu canjin manhajar karatu a kasashen larabawan da suke bin tafarkin akidar wahabiyanci ba, to kuwa dakushe kaifin tsatsauran ra'ayi da ta'addanci a cikin kasashen musulmi, zai zama mai matukar wahala, musamman idan aka yi la'akari da irin yadda kasashen da suke bin wannan akida suka yi tasiri da kuma yin kutse a mafi yawan kasashen musulmi.
Da dama daga cikin masana sun yi imanin cewa, ko shakka babu, yadda kasashen yammacin turai har ma da yahudawan sahyuniya suke mara baya ga kasashen larabawan da ke yada irin wanann akida da ke haifar da ta'addanci, shiryayyen lamari ne da ake nufin yin amfani da shi domin bata sunan addinin muslunci da kuma rusa kasashen musulmi, da kuma karfafa samuwar Haramtacciyar Kasar Isra'ila a yankin gabas ta tsakiya, tare cimma wasu bakaken manufofi na siyasa a kan kasashen na musulmi ta hanyoyi daban-daban, musamman ma gwamnatocin musulmi da na larabawa da ba su yin amshin shata ga kasashen yammacin turai.
Babban misalin da masu wannan ra'ayi suke kafa hujja da shi, shi ne irin rawar da Amurka da Birtaniya suka taka wajen kafa kungiyoyin 'yan ta'adda irin su Alqaeda, Taliban, da kuma yadda suka yi amfani da malaman kasashen da ke bin akidar wahabiyanci wajen karfafa wadannan kungiyoyi da fatawoyi domin tunzura su zuwa ga aikata ta'addanci da sunan muslunci, wanda hakan kuma shi ne babban makamin da Amurka da Birtaniya suka yi amfani da shi wajen rusa kasashen Afghanistan da Iraki, kamar yadda kuma a halin yanzu suke yin amfani da wadannan kungiyoyin 'yan ta'adda da sunaye daban-daban wajen rusa kasashen Syria, Libya da sauransu.