Syria: Afuwa Ga Duk Wanda Ya Ajiye Makamansa
(last modified Sat, 10 Mar 2018 19:01:03 GMT )
Mar 10, 2018 19:01 UTC
  • Syria: Afuwa Ga Duk Wanda Ya Ajiye Makamansa

Sojojin Syria da suke yaki da 'yan ta'adda a yankin Ghuda ne suka yi sanarwar yin afuwa ga duk wanda ya ajiye makamansa

Sojojin na Syria suna ci gaba da samun galaba akan 'yan ta'addar da suke a yankin na Ghuda inda a bayan nan suka kwace iko da yankin Aftaris, da kuma wani sashe Hush al-Ashari.

Tashar talabijin din al'alam ta bakin dan rahotonta a Syria Husain Murtadha ya ambato majiyar sojan kasar na cewa: Za su bude hanyoyin da 'yan ta'addar za su iya ficewa cikin aminci idan har suka ajiye makaman nasu.

A wani labari, tashar talabijin din Al-akhbar ta gwamnatin Syria ta ce; sojojin kasar sun kwato fararen hula 60 da 'yan ta'adda suke garkuwa da su a yankin Misrabah na Ghuda. A yau asabar ne dai sojojin Syria suka kwace iko da yankin na Misrabah, daga karkashin ikon 'yan ta'adda.