Sojojin Siriya Na Shirin Kawo Karshen 'Yan Ta'adda A Yankin Douma
Dakarun kasar Siriya na shirin kai farmakin kakkabe 'yan ta'addar dake jibke a Douma na yankin Ghouta dake gabashi birnin Damuscus.
Tashar talbijin din almayadin ta habarta cewa Sojojin kasar Siriya na jiran umarni na kai farmaki cikin garin Douma bayan da wa'adin da aka bawa mayakan 'yan ta'adda na su fice daga cikin garin ya kwo karshe, a gefe guda al'ummar garin ke gudanar da jerin gwano na bukatar dakarun tsaron kasar su gaggauta ciga cikin garin domin tsarkake shi daga 'yan ta'addar.
A cewar tashar talbijin din Almayadin din kungiyar 'yan ta'adda na Jaishu-Islam dake cikin yankin na Douma sun nuna rashin amincewarsu magance matsalar cikin ruwan sanyi inda suka gindaya sharadin ficewa da dala miliyan dari tara zuwa yankin kalamun na gabas, sharadin da dakarun kasar Siriya suka yi watsi da shi.
Al-Baidawi shugaban kungiyar 'yan ta'addar na Jaishil-islam da kasar Saudiya ta kafa, a jiya laraba ya aike da sako ga gwamnatin kasar Siriya na cewa ba za su amince da fita daga garin na Douma ma ba tare da sojojin kasar sun amince da sharadin su ba.