Amerika: An Kai karar Saudiyya Akan Harin 11 Ga Satumba
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i29708-amerika_an_kai_karar_saudiyya_akan_harin_11_ga_satumba
Iyalan wadanda aka kashe a harin 11 ga watan Satumba sun kai Saudiyya kara a kotun kasar Amurka.
(last modified 2018-08-22T11:31:40+00:00 )
Apr 07, 2018 18:08 UTC
  • Amerika: An Kai  karar Saudiyya Akan Harin 11 Ga Satumba

Iyalan wadanda aka kashe a harin 11 ga watan Satumba sun kai Saudiyya kara a kotun kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ce; A ranar litinin mai zuwa ne dan majalisar dattijai Richard Blumenthal, tare da iyalan wadanda aka kashe a harin, za su tsaya  a gaban ginin kotun koli ta Amurka domin bayyanawa duniya matakin da su ka dauka na kai karar Saudiyya.

Iyalan mutane suna zargin gwamnatin Saudiyyar ne da cewa tana da hannu a harin na 11 ga watan Satumba.Mutane 15 daga cikin maharan 19 sun fito ne daga kasar Saudiyya.

A shekarar 2016 ne aka yi doka a Amurka wacce ta ba da damar a kai karar gwamnatin wata kasa a kotun Amurka bisa wani laifi da su ka aikata.