Faransa: Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado Ya Gana Da Shugabar MKO
Muhammad Bin Salman ya gana da jagorar kungiyar MKO mai adawa da tsarin musulunci a Iran Maryam Rajabi, a gidansa da ke birnin Paris
Yariman na Saudiyya ya jinjinawa kungiyar ta munafikai akan rawar da suka taka a tashe-tashen hankulan da su ka faru a yammacin kasar Iran a shekarar da ta gabata, sannan ya jaddada cewa za su gaba da bai wa kungiyar tallafin kudade.
Mambobin kungiyar ta MKO da dama sun yi gangami a bakin ginin ma'aikatar harkokin wajen Faransa domin nuna goyon bayansu ga ziyarar da yariman na Saudiyya ya kai kasar ta Faransa.
A cikin kwanakin nan ne Maryam Rajabi ta yi hira da jaridar Ukkaz ta Saudiyya da a ciki ta bayyana cewa; Kungiyarta ta taka rawa a tashe-tashen hankulan da su ka faru a yammacin kasar Iran a shekarar da gabata.