Kungiyar "Amnesty" Ta Bukaci A Gudanar Da Binciken Kisan Palasdinawa
Kungiyar kare hakkin bil'adaman ta kasa da kasa daga ofishinta da ke birnin London ta bukaci da a gudanar da bincike mai cin gashin kanshi dangane da amfani da karfi akan al'ummar Palasdinu da 'yan sahayoniya su ke yi.
Kiran na kungiyar kare hakkin bil'adaman ya zo ne a lokacin da Zanga-zangar Palasdinawa ta hakkin komawa zuwa kasarsu ta gado, ya shiga mako na uku a jere.
Shugaban shashen yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka na kungiyar kare hakkin bil'adam ta Amnesty International Midalna Magaribi ya bayyana yadda a cikin shekaru uku na bayan nan sojojin haramtacciyar Kasar Isra'ila suke keta hurumin palasdinawa da yi musu kisan gilla, da su ka hada kananan yara.
Jami'in ya ci gaba da cewa; Wajibi ne yan sahayoniyar su gaggauna kawo karshen wannan siyasar tasu.