Masar Ta Ki Amincewa Da Aika Sojoji Zuwa Kasar Syria
Wani babban jami'in leken asirin Masar ya ce; Babu yadda za a yi Masar ta shiga cikin kawancen fada da Syria
Tashar talabijin din Euro Newa ta ambato Muhammad Rashad yana mai da martani akan bukatar da John Bulton ya bijiro wa da Masar shi akan aika sojoji zuwa kasar Syria domin maye gurbin sojojin Amurka.
Rashad ya ci gaba da cewa; Siyasar kasar Masar dangane da Syria shi ne ci gaba da zamanta dunkulalliya a karkashin jagoranci guda.
Tun da fari ministan harkokin wajen saudiyya Adil Jubair ya ce kasarsa za ta aike da sojoji zuwa kasar Syria a karkashin abin da ya kira kawancen kasashen musulmi na fada da ta'addanci.
Jaridar Wall Street Journal ta cel Amurka tana son ganin larabawa sun aike da sojoji domin su maye gurbinta idan ta fice daga Syria.