OPCW Ta Gama Bincikenta A Garin Duma Na Siriya
Kungiyar haramta amfani da makamai masu guba ta duniya, (OPCW), ta ce tawagar da ta tura Siriya, dangane da zargin da aka yi wa kasar, na amfani da makamai masu guba wajen kai hari kan fararen-hula, ta kammala bincikenta a garin Duma.
Sanarwar da kungiyar ta fitar jiya, ta ce tawagar ta tattara wasu bayanai a garin Duma, ciki har da wasu sinadaran da ta gano a wurin, wadanda ta riga ta tura zuwa dakin gwaje-gwaje na kungiyar don gudanar da bincike.
Binciken dai zai dauki tsawon mako ukku zuwa hudu.
A ranar 7 ga watan Afrilun wannan shekara da muke ciki ne, aka yi amfani da makamai masu guba wajen kai hari garin Duma dake yankin gabashin Ghouta na kasar Siriya, kuma kwanaki kadan bayan hakan kasashen da suka da Amurka, Biritaniya da Faransa suka kai wa Siriya hari bisa zarginta da kai harin na Duma.
Gwamnatin Siriya dai ta musanta zargin har ma ta gayyaci kungiyar ta OPCW don tura tawagarta zuwa garin Duma da nufin gudanar da bincike, amma duk da hakan kasashen suka yi gaban kansu wajen kai mata harin jiragen sama, ba tare da amuncewar kwamitin tsaro MDD ba.