Bahrain: Jami'an Tsaro Sun Kai Hari Akan Gidajen Fararen Hula
Kwanaki biyu ajere kenan da jami'an tsaron gwamnatin Bahrain suke kai wa gidajen fararen hula hari tare da yin barna a cikinsu
Kungiyar 'yan hamayyar siyasar kasar ta Bahrain, al-wifaq ta yi tir da harin tana mai cewa; A jiya laraba kadai jami'an tsaron sun kai hare-hare har sau 13 a cikin unguwanni daban-daban na kasar tare da kame mutane 15.
A daren jiya wanda shi ne daren farko na watan Ramadhan, jami'an tsaron sun kame mata biyu a unguwar al-nuwaidarat.
Sai dai a yau alhamis mazauna yankunan al-nuwaidirat da al-akar da almaamir sun fito Zanga-zangar nuna kin amincewa da kamen da jami'an tsaron suke yi wa mutane.
Al'ummar Bahrain sun yunkura da zummar neman sauyi a fagen siyasar kasar tun a ranar 14 ga watan Febrairu na 2011.