Bahrain: Jami'an Tsaro Sun Kai Hari Akan Gidajen Fararen Hula
(last modified Thu, 17 May 2018 18:52:48 GMT )
May 17, 2018 18:52 UTC
  • Bahrain: Jami'an Tsaro Sun Kai Hari Akan Gidajen Fararen Hula

Kwanaki biyu ajere kenan da jami'an tsaron gwamnatin Bahrain suke kai wa gidajen fararen hula hari tare da yin barna a cikinsu

Kungiyar 'yan hamayyar siyasar kasar ta Bahrain, al-wifaq ta yi tir da harin tana mai cewa; A  jiya laraba kadai jami'an tsaron sun kai hare-hare har sau 13 a cikin unguwanni daban-daban na kasar tare da kame mutane 15.

A daren jiya wanda shi ne daren farko na watan Ramadhan, jami'an tsaron sun kame mata biyu a unguwar al-nuwaidarat.

Sai dai a yau alhamis mazauna yankunan al-nuwaidirat da al-akar da almaamir sun fito Zanga-zangar nuna kin amincewa da kamen da jami'an tsaron suke yi wa mutane.

Al'ummar Bahrain sun yunkura da zummar neman sauyi a fagen siyasar kasar tun a ranar 14 ga watan Febrairu na 2011.